Shirin cigaban aikin noma da kiwo na Jihar Kano (KSADP), ya fara horar da matasa 1,000 a kan yadda za a sarrafa ciyawar shinkafa domin amfani da ita a matsayin abincin dabbobi.
Bayanin hakan na cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na shirin KSADP, a jihar Kano Ameen Kabeer Yassar, ya fitar.
Shugaban aikin na KSADP, Malam Ibrahim Garba Muhammad, ne ya bayyana hakan a yayin kaddamar da horon da ake gudanarwa a Kwalejin Noma ta Audu Bako da ke Dambatta. Ya ce wannan shiri na samun tallafi daga Bankin Raya Musulunci da kuma shirin (LLF), da nufin samar da ayyukan yi da hanyoyin samun kudin shiga ga matasan da yawancinsu suka fito daga yankunan da ake noma shinkafa a jihar Kano.
Ya ce, wannan horo kan amfani da ciyawar shinkafa na da matuƙar muhimmanci wajen inganta noma mai ɗorewa da kuma samar da damarmaki na tattalin arziki.
Ta hanyar koya wa matasa yadda za a yi amfani da ciyawar shinkafa maimakon kona ta kamar amfani da ita wajen yin takin zamani ko ciyar da dabbobi inda hakan zai rage gurbatar muhalli tare da ƙara samun kudin shiga.
Malam Ibrahim ya kara da cewa, idan abincin dabbobi ya samu yawaitar da za a iya dogaro da shi daga gonakin shinkafa na cikin gida, hakan zai rage yawan yawo da dabbobi wanda a wasu lokuta ke haddasa matsalolin tsaro. Haka kuma zai inganta dangantaka tsakanin manoma da makiyaya a jihar Kano.
KSADP na shirin kafa cibiyoyi 200 na sarrafa ciyawar shinkafa a kusa da yankunan da ke da shirin ban ruwa, tare da bai wa kowanne rukuni tallafi ko bashin kayan aiki, injina da hanyoyin jigila don samar da abincin dabbobi daga ciyawar shinkafa da aka sarrafa.
A nasa jawabin, Shugaban Kwalejin Noma ta Audu Bako, Farfesa Muhammad Wailare, ya bayyana jin daɗin hadin gwiwar da suka yi wajen shirya horon, inda ya ce za a koya wa matasan dabarun amfani da ciyawar shinkafa ta hanyoyi masu sauƙi da za su ba su damar samun kudin shiga, su kuma inganta noma mai dorewa da rage gurbatar muhalli.