Dakatacciyar Sanata mai wakiltar Mazabar Kogi ta tsakiya Natasha Akpoti-Uduaghan, ta isa Kotun Babban Birnin Tarayya da ke Maitama, Abuja, domin gurfana a gaban kuliya kan zargin bata suna.
Sanata Akpoti-Uduaghan ta shiga cikin kotu da misalin ƙarfe 10:30 na safe, kafin zaman kotu da aka shirya farawa da ƙarfe 11:00, inda ake jiran zuwan alkalin da zai jagoranci sauraren shari’ar.
Babban Daraktan Ɗaukar Nauyin Gurfanar da Masu Laifi na Ƙasa, Mohammed Abubakar, ne ya shigar da ƙarar a madadin Gwamnatin Tarayya a kan Sanata Akpoti-Uduaghan.
A cikin ƙarar mai lamba CR/297/25, Gwamnatin Tarayya ta zargi Sanatar da yin maganganu masu cin mutunci da suka shafi Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, a wani shirin talabijin da aka watsa kai tsaye.
Sanarwar ƙarar ta bayyana Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, da tsohon Gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello, a matsayin masu kai ƙorafi a shari’ar.
An zargi Sanatar da cewa ta bayyana a fili cewa Yahaya Bello ya haÉ—a baki da Akpabio domin shirya mata kisan kai a wajen birnin Abuja.
Gwamnatin Tarayya ta ce Sanatar ta yi wannan zargi ne a wani shirin Politics Today na talabijin yChannels a ranar 3 ga Afrilu, 2025.
A cewar Gwamnatin Tarayya, Sanatar ta yi waɗannan kalamai ne da gangan ko da rashin kulawa, tare da sanin cewa hakan zai iya ɓata suna da mutuncin waɗanda abin ya shafa.