Namadi Sambo ya musanta ficewar sa daga PDP 

0
24

Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Alhaji Mohammed Namadi Sambo, ya karyata jita-jitar da ke yawo cewa ya sauya sheƙa zuwa jam’iyyar APC, yana mai jaddada cewa har yanzu yana nan daram a matsayin ɗan jam’iyyar PDP.

:::Cikakken tarihin Jagoran Addini na ƙasar Iran, Ayatollah

A wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Malam Umar Sani, ya fitar a ranar Laraba, Sambo ya bayyana jita-jitar da ke yawo a kafafen sada zumunta a matsayin ƙarya ce maras tushe, wacce aka kirkira domin yaudarar jama’a da janyo ruɗani.

Sanarwar ta yi bayani cewa hoton da ake ta yadawa wanda ya nuna Sambo tare da Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ba sabo ba ne, tsohon hoto ne da aka ɗauka shekaru da suka wuce lokacin da Gwamnan ya kai masa ziyara ta jaje a gidansa da ke Abuja, bayan rasuwar ɗan uwansa, marigayi Sani Sambo.

“Wasu ke ƙoƙarin amfani da hoton wajen yaudarar jama’a da ƙirƙirar labarin da ba shi da tushe ko makama,” in ji sanarwar.

Haka kuma, sanarwar ta bayyana cewa halartar da Namadi Sambo zai yi wajen kaddamar da gadajen asibiti 300 a Kaduna a ranar 19 ga Yuni, 2025, ba yana nufin sauya sheƙa ba ne, ko nuna goyon baya ga wata jam’iyya ta siyasa.

A cewar sanarwar, Sambo shi ne ya fara wannan aikin asibitin, kuma hakan wani bangare ne na gudummawarsa ga ci gaban jihar Kaduna da walwalar jama’a.

“Babu wani yunƙuri daga Alhaji Namadi Sambo na sauya sheƙa zuwa kowace jam’iyya,” sanarwar ta jaddada.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here