ASUU ta maka gwamnatin tarayya a kotu saboda yiwa kishiyoyinta rajista 

0
82

Kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) za ta tunkari kotun ma’aikata kan lamarin da gwamnati ta gabatar na yiwa kungiyoyin dake kishiyantarta rajista.

Lauyan ASUU, Femi Falana ne ya shaidawa Channels Tv cewa, kungiyar za ta tunkari kotun ma’aikata domin kai kokenta.

Hakazalika, shugaban kungiyar Farfesa Emmanuel Osodeke ya tabbatar da hakan a wata tattaunawa da aka yi dashi a ranar Alhamis 6 ga watan Okotoba.