Jami’ar ABU ta haramtawa ma’aikata da ɗalibai runguma da sanya suturar da bata dace ba

0
175

Jami’ar ABU ta haramtawa ma’aikata da ɗalibai runguma da sanya suturar da bata dace ba

Jami’ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zariya tayi dokar da ta janyo cece-kuce daga ɗalibai da ma’aikata bayan da ta fitar da sabuwar dokar sanya sutura wadda ta haramta sanya wando ko siket gajere, kaya masu matse jiki, ƙarin gashin gira (eyelashes) da ma runguma a harabar jami’ar.

Wannan doka ta bayyana ne a cikin wata sanarwa ta musamman da ta fito ranar 16 ga Yuni, wadda shugabancin jami’ar ya rattaba wa hannu. Sanarwar ta bayyana jerin abubuwan da jami’ar ke kallon su a matsayin “sutura marar dacewa da kuma abin ƙyama”, tare da gargadin cewa duk wanda ya karya wannan doka zai fuskanci hukunci.

A cewar sanarwar, dokar ta shafi ɗaukacin ɗalibai da ma’aikata, inda aka haramta sanya kaya da suka bayyana sassa na jiki ko kuma waɗanda ba su dace da muhalli na ilimi ba.

Daga cikin kayayyakin da aka hana akwai rigunan da ke da igiyar hannu, kaya masu bayyana fata (see-through), wanduna da riguna masu tufa ko rami, siket da wandunan da ke ƙasa da gwiwa (banda na motsa jiki), da kaya masu matse jiki ko waɗanda ke hana amfani da kayan dakin gwaji (lab coat) yadda ya kamata.

Haka kuma, an haramta wa ɗaliban maza sanya ‘yan kunne, da sarka a ƙafa ga ɗaliban mata, gashin gira. Haka zalika, maza ba su da damar nadewa ko kitse gashinsu.

Sanarwar ta kuma bayyana cewa jami’ar ba za ta yarda da barin gashi ko gemu da yawa da yawa ba.

Sabuwar dokar ta kuma haramta nuna soyayya a fili kamar runguma, sumbata, da zama a jikin juna. Sauran abubuwan da aka bayyana a matsayin doka sun haɗa da sanya rigunan da ke ɗauke da saƙonnin banza, wando da ya tsaya a tsakiyar ƙafa, tabarau masu launi, da kuma sanya hula ta hanyar da ba ta dace ba.

Sai dai wannan sabon tsarin ya jawo suka daga wasu ɗalibai da ma’aikata.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here