Mutane 700 sun ɓace sakamakon ambaliyar Mokwa a jihar Neja

0
97

Mutane 700 sun ɓace sakamakon ambaliyar Mokwa a jihar Neja

Gwamnatin Jihar Neja ta bayyana cewa mutane sama da 700 har yanzu ba a san inda suke ba, bayan ambaliyar da ta shafi al’ummar Mokwa da ke Karamar hukumar Mokwa.

Gwamna Umaru Bago na Jihar Neja ne ya bayyana hakan a ranar Talata, yayin da yake karɓar ziyarar tsohon jami’in tsaro na marigayi Janar Sani Abacha, Manjo Hamza Al-Mustapha tare da abokansa, waɗanda suka kai masa ziyarar ta’aziyya bisa ambaliyar.

Gwamna Bago, wanda Mataimakinsa Yakubu Garba ya wakilta, ya kuma bayyana cewa an tabbatar da mutuwar mutane 207, yayin da iyalai sama da 3,000 suka rasa muhalli.

“Mutane fiye da 700 har yanzu ba a san inda suke ba, kuma har yanzu ba mu gano inda suka shiga ba. Ambaliyar ta jawo mummunan barna sosai,” in ji shi.

Ya bayyana cewa ambaliyar ta lalata gidaje kusan 400, yayin da gidaje 283 da shaguna 50 suka rushe gaba ɗaya.

Ya kuma bayyana cewa gwamnatin jihar tana aiki da ƙwararrun ƙungiyoyi domin gano musabbabin ambaliyar, kuma suna jiran sakamakon binciken.

A nasa jawabin Al-Mustapha, yace sun ziyarci jihar Neja don jajantawa al’umma da gwamnati akan iftila’in ambaliyar data afku.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here