Isra’ila ta kashe Falasɗinawa 60 lokacin da suke karɓar tallafin abinci

0
24

Isra’ila ta kashe Falasɗinawa 60 lokacin da suke karɓar tallafin abinci

Shaidu da ma’aikatan ceto sun tabbatar da cewa sojojin Isra’ila sun buɗe wuta kan Falasɗinawa da ke taruwa domin karɓar garin fulawa a kusa da sansanin raba kayan tallafi da ke Khan Younis, cikin Zirin Gaza.

Rahotanni sun bayyana cewa sama da mutane 200 ne suka jikkata a sakamakon wannan hari da dakarun Isra’ila suka kai.

Harin na a matsayin ɗaya daga cikin munanan hare-haren da aka kai kan fararen hula da ke kokarin samun abinci a Gaza cikin jerin hare-haren baya-bayan nan da Isra’ila ke kaiwa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here