Alkairai ne suka zo Rimin Zakara ba rusau ba—Masanin harkokin filaye 

0
88

Shugaban kungiyar masu sana’ar siyar da filaye gidaje da Kango, Alhaji Naziru Tijjani Idris, yace babu batun yin rusau a garin Rimin Zakara, biyo bayan sanya jan fenti a gidaje da Kangwaye a gidajen garin.

Alhaji Naziru, wanda shine mamallakin kamfanin Annatija Properties, yace alamun jan fenti da aka gani gwamanti ta saka shaida ce ta ƙirg gidaje da Kango don samar da alkairai ga al’ummar Rimin Zakara, tare da cewa babu abinda zai sanya gwamnatin Kano yin rusau a garin.

Ya ƙara da cewa hakan zai zama nasara ga al’ummar dake rayuwa a garin biyo bayan alƙawarin gwamna Abba Kabir Yusuf, na ƙoƙarin samar da cigaba mai ɗorewa a yankin.

Yayi kira ga al’ummar wanan yankin dasu sani cewa Idan za’a yi rusau ana rubuta alamar cewa rushe waje za’a yi, amma wanan kuma alamace ta kidayar gidaje da kwangwaye domin cigaban da tallafawa mazauna yankin 

Alh Naziru Tijjani Annatija, yace idan mutane zasu tuna a baya gwamnan Kano, yayi alkawarin kawo wutar lantarki yankin da asibiti da makaranta harma da masallacin Juma’a, yana mai cewa a halin Yanzu kullum ma’aikatan gwamnnatin suna zuwa yankin don cigaba da kawo ayyukan alkhairi.

A karshe yace don haka masu gidaje da filaye da kwangwaye a Rimin Zakara su kwantar da hankalinsu babu komai da zai faru sai dai alkairi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here