Najeriya ta rage shigo da fetur daga ƙasashen waje

0
107
man fetur
man fetur

Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa (NBS) ta bayyana cewa an samu gagarumar raguwar kuɗin da Najeriya ke kashewa wajen shigo da man fetur daga ƙasashen waje, inda aka ajiye sama da naira tiriliyan biyu a tsakanin shekarar da ta gabata da yanzu.

A cikin wani rahoto da hukumar ta fitar, NBS ta ce a zangon farko na shekarar da ta gabata, Najeriya ta kashe naira tiriliyan 3.81 wajen shigo da man fetur. Amma a zangon farko na 2025, wannan adadin ya ragu da kashi 54 cikin 100.

Hukumar ta danganta wannan raguwar ne da ƙaruwar samar da man fetur a cikin gida, musamman daga matatar man Dangote, wadda ta fara aiki a baya-bayan nan. Wannan matata ta taka rawar gani wajen saukaka dogaro da shigo da man daga ƙasashen waje.

Binciken hukumar ya kuma nuna yadda shigo da fetur ya rika ƙaruwa daga 2020 zuwa 2024. A zangon farko na 2020, Najeriya ta shigo da man fetur na kimanin naira biliyan 732. Wannan adadin ya tashi zuwa tiriliyan 1.29 a 2021, sannan ya ninka zuwa tiriliyan 2.69 a 2022, har ya kai tiriliyan 3.81 a 2024.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here