Ina Jin daɗin ikicin da Jam’iyyun adawa ke ciki—TINUBU

0
68

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana farin cikinsa kan rikice-rikicen da jam’iyyun adawa ke fama da su a halin yanzu.

Da yake jawabi yayin bikin ranar Dimokuraɗiyya da aka gudanar a zauren majalisar dokoki da ke Abuja, ranar Alhamis, Tinubu ya ce yana ganin hakan a matsayin wata alama ta karfafa jam’iyyar sa ta APC.

“Ina jin daɗin ganin jam’iyyun adawa a tagayyare. Ba zan ce ina so na ga kun gyaru ba, ina ma jin daɗin ganin ku a haka,” in ji Tinubu.

Jawabin nasa na zuwa ne a daidai lokacin da jam’iyyar APC ke ci gaba da karɓar sabbin ‘yan siyasa da ke sauya sheƙa daga jam’iyyun adawa zuwa cikinta.

Tinubu ya ce ko shakka babu, jam’iyyar sa ba za ta hana kowa shiga cikinta ba, domin hakan zai sabawa ƙa’idar dimokuraɗiyya da kuma hakkin ‘yan ƙasa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here