Tinubu ya Karrama wasu fitattun ƴan Najeriya da lambobin girmamawa 

0
38

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya karrama wasu fitattun ’yan Najeriya da lambobin girmamawa na shugaban ƙasa, bisa gudummawar da suka bayar wajen haɓaka dimokuraɗiyya, kare haƙƙin ɗan adam da ci gaban ƙasa.

An sanar da waɗannan lambobin girmamawa ne a zaman haɗin gwiwa na Majalisar dokokin Ƙasa da aka gudanar a ranar 12 ga Yuni, a wani ɓangare na bikin ranar dimokuraɗiyya a Najeriya.

Daga cikin waɗanda aka karrama, akwai marigayiya Kudirat Abiola, wadda aka bai wa lambar girmamawa ta (CFR). Kudirat, wadda ta kasance jaruma mai rajin dimokuraɗiyya kuma matar marigayi Chief Moshood Kashimawo Olawale (MKO) Abiola, wanda ta taka rawar gani a fafutukar dawo da mulkin dimokuraɗiyya bayan soke zaɓen shugaban ƙasa na 1993 zaɓen da akasarin ’yan Najeriya suka yarda mijinta ne ya ci.

Sauran waɗanda aka karrama sun haɗa da:

Bola Ige (CFR) – Tsohon Ministan Shari’a kuma gogaggen mai fafutukar dimokuraɗiyya.

Pa Reuben Fasoranti (CFR) – Dattijo kuma jagoran kungiyar Afenifere.

Nurudeen Olowokere (CON) – Bisa gudummawarsa ga tsarin dimokuraɗiyya.

Farfesa Wole Soyinka (GCON) – Mashahurin marubuci wanda aka karrama bisa jajircewarsa wajen kare adalci da haƙƙin ɗan adam.

Farfesa Olatunji Dare (GCON) – Mashahurin ɗan jarida, malami da masanin ilimi.

Bayo Onanuga (CON) – Gogaggen ɗan jarida kuma mai ba shugaban ƙasa shawara, wanda aka karrama bisa rawar da ya taka wajen jaridar da ke goyon bayan dimokuraɗiyya.

Sanata Shehu Sani (CON) – Tsohon sanata kuma mai rajin kare haƙƙin ɗan adam, wanda aka karrama bisa aikin sa a cikin al’umma.

Femi Falana (CON) – Mashahurin lauya mai kare haƙƙin ɗan adam da ƙwararren masani kan kundin tsarin mulki.

Yayin da yake jawabi a wajen bikin, Shugaba Tinubu ya bayyana cewa wadannan lambobi sun nuna yadda Najeriya ke girmama wadanda suka tsaya tsayin daka wajen kare gaskiya, adalci da akidar dimokuraɗiyya a kowane hali.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here