Gwamnatin tarayya ta soke faretin sojoji na ranar dimokuraɗiyya

0
39

Gwamnatin arayya ta soke gudanar da faretin sojoji na shekara-shekara da ake yi domin bikin Ranar dimokuraɗiyya, wanda aka shirya gudanarwa a ranar Alhamis, 12 ga Yuni, 2025.

Kwamitin haɗin gwiwa na ma’aikatun gwamnati wanda ke da alhakin tsara shirye-shiryen bikin Ranar dimokuraɗiyya ne ya sanar da hakan, inda ya tabbatar da cewa ba za a gudanar da faretin ba kamar yadda aka saba yi a shekarun baya.

A maimakon haka, bikin bana zai fara ne da jawabin shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu da safe, ƙarfe 7:00 na safe, inda ake sa ran zai yi bitar tafiyar dimokuraɗiyyar Najeriya, ya yi bayani kan halin da ƙasar ke ciki, da kuma shirye-shiryen gyare-gyaren da ake aiwatarwa don ƙarfafa cibiyoyin dimokuraɗiyya da inganta shugabanci nagari.

Da misalin ƙarfe 12:00 na rana, shugaban ƙasa zai halarci wani zama na musamman tare da majalisar dokoki ta ƙasa, inda za a tattauna ci gaban dimokuraɗiyya a ƙasar, haɗin kan ƙasa, da ƙoƙarin inganta muhimman sassa na gwamnati domin samar da shugabanci nagari.

Bayan haka, za a gudanar da babban taron ilimi da misalin ƙarfe 4:00 na yamma a Dandalin Taro na Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja. Taken taron shi ne “Ƙarfafa Dimokuraɗiyya Ta Hanyar Gyare-gyare Masu Dorewa”, inda manyan ‘yan siyasa, masu tsara manufofi da wakilan ƙungiyoyin farar hula za su bayyana ra’ayoyinsu game da ci gaban dimokuraɗiyya da ƙalubalen da ke tattare da ita.

Ko da yake babu wani cikakken bayani da aka fitar kan dalilin soke faretin, wata majiya daga fadar shugaban ƙasa ta bayyana cewa hakan na iya nasaba da abin da ya faru a bara, inda shugaban ƙasa Tinubu ya yi tuntuɓe yayin da yake ƙoƙarin hawa motar faretin a Dandalin Eagle da ke Abuja.

Duk da cewa lamarin ya jawo ce-ce-ku-ce a lokacin, shugaban ya dawo hayyacin sa cikin gaggawa kuma ya ci gaba da gudanar da bikin.

Duk da jita-jita, jami’an gwamnati sun tabbatar da cewa lafiyar shugaban ƙasa ƙalau, kuma yana da cikakkiyar niyya wajen ci gaba da tafiyar da manufofin dimokuraɗiyya a Najeriya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here