Kungiyar Matan ƴan Sanda ta Jihar Kano (POWA), ƙarƙashin jagorancin Hajiya Hadiza Abubakar Bakori, ta kai ziyara Gidauniyar marayu na Nassarawa inda ta raba kayan abinci, tufafi, raguna da wasu kayan tallafi ga marayu da yara masu buƙata ta musamman.
Ziyarar ta gudana ne a ranar Lahadi, 9 ga Yuni, 2025.
A cewar sanarwar da Jami’in hulɗa da Jama’a na Rundunar ‘Yan Sanda ta Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar, wannan tallafi wani ɓangare ne na ƙoƙarin kungiyar POWA wajen taimaka wa yara marasa galihu.
An hangi Hajiya Hadiza tana mu’amala da yara da ma’aikatan gidan, sannan tana mika musu kayan tallafi da kuma tattaunawa da su.
Mallam Muhammad Sambo Iliiyasu, wanda ya wakilci Kwamishinan ma’aikatar harkokin mata, yara da Nakassu, shi ne ya karɓi kayan tallafin a madadin ma’aikatar.
“Muna matuƙar godiya ga POWA bisa wannan kyautar da suka bayar da kuma yadda suke nuna damuwa da jin ƙai ga al’umma,” in ji Mallam Iliiyasu.
“Rundunar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano na yabawa POWA bisa wannan kyakkyawar gudummawa, kuma tana ƙarfafa sauran ƙungiyoyi da mutane masu hannu da shuni su rika aiwatar da irin waɗannan ayyuka na jin ƙai don tallafa wa marasa ƙarfi,” in ji sanarwar.