Ganduje ya jajantawa ƴan kasuwar Farm Centre akan gobarar da suka yi

0
43

Shugaban jam’iyyar  APC na ƙasa, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana alhininsa tare da jajanta wa ‘yan kasuwa da mazauna yankin da gobarar da ta tashi a babbar kasuwar wayar hannu ta Farm da ke jihar Kano ta shafa.

Bayanin hakan cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Ganduje Edwin Olofu, yace shugaban jam’iyyar, ya bayyana wannan gobara a matsayin babban rashi ba kawai ga ‘yan kasuwar da suka yi asarar kayayyaki da dukiyoyinsu ba, har ma ga tattalin arzikin jihar Kano da na ƙasa baki ɗaya.

Wannan kasuwa cibiya ce ta kasuwanci, kirkire-kirkire, da bayyana ƙwazon matasa. asarar da aka yi ta dukiya abin takaici ne matuƙa, in ji Ganduje.

Ya bukaci hukumomin da abin ya shafa na jiha da na tarayya, da su gaggauta binciken musabbabin gobarar da kuma ɗaukar matakan tallafi na gaggawa da na dogon lokaci ga waɗanda lamarin ya rutsa da su.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here