Magoya bayan APC na Kano sun goyi bayan Tinubu ya yi tazarce

0
112

Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin, tare da daukacin magoya bayan jam’iyyar APC na Arewacin Kano, sun bayyana cikakken goyon bayansu ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu domin ya sake tsayawa takara a zaben shekara ta 2027.

Sanata Barau ya bayyana hakan ne yayin bikin kaddamar da sauya makarantar Federal Polytechnic, Kabo zuwa Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Tarayya, Kabo a ranar Talata, bayan amincewar Shugaba Tinubu da bukatar da Sanatan ya mika masa a baya.

A yayin taron da aka gudanar a karamar hukumar Kabo ta jihar Kano, daruruwan magoya bayan jam’iyyar APC da masoya Sanata Barau sun halarta tare da nuna farin cikinsu da godiya ga shugaban kasa.

“Aikin da Shugaba Tinubu ke yi da soyayyarsa ga yankin Sanatan Kano ta Arewa ya isa ya tabbatar da goyon bayan mu ga ci gaba da mulkinsa bayan 2027,” in ji Sanata Barau.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here