Muna samun nasara a yaƙi da kungiyar Boko Haram—Gwamnatin tarayya

0
49

Ministan tsaro Badaru Abubakar ya tabbatar da dawowar hare-haren Boko Haram a Arewa Maso Gabas, musamman jihar Borno, yana mai cewa hakan wani ɓangare ne na shirin tayar da hankali da mayakan ke yi a yankin Sahel, wanda ke shafar ƙasashen Najeriya, Mali, Burkina Faso da Jamhuriyar Nijar.

Yayin wata ganawa da manema labarai a Kaduna bayan wata ziyarar kwanaki biyu da ya kai cibiyoyin soji a jihar, Badaru ya bayyana cewa gwamnatin tarayya na ɗaukar matakai na gaggawa don tinkarar barazanar.

“A cikin makonni biyu da suka gabata, dakarunmu sun sami gagarumar nasara wajen kawar da adadi mai yawa na ‘yan ta’adda,” in ji shi.

A yayin ziyarar, ministan ya zagaya tsohuwa da sabuwar makarantar horar da sojoji ta NDA.

Dangane da rikicin Benue, ya bayyana cewa rikicin manoma da makiyaya ne, wanda ke buƙatar hanyoyin warware matsala ba tare da amfani da karfi ba, ciki har da shiga tsakani da sulhu tsakanin al’umma.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here