Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya tabbatar da matsayarsa ta siyasa, yana mai cewa zai jagoranci yakin neman zaɓen sake zaɓen Shugaba Bola Tinubu a jihar Ribas, duk da kasancewarsa babban jigo a jam’iyyar adawa ta PDP.
Wike, a baya ya taɓa riƙe Gwamnan Jihar Ribas, ya bayyana hakan ne a wata hira da manema labarai da aka yi da shi a birnin Abuja a ranar Litinin.
A yayin hirar, ya ce a zaɓen 2027, biyayyarsa za ta kasance ga Shugaba Tinubu, ba wai ɗan takarar shugaban ƙasa na PDP ba.
Wike, wanda ya kammala wa’adinsa a matsayin gwamnan Ribas a shekarar 2023, ya nuna goyon bayansa ga Tinubu wanda a wancan lokacin shi ne ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar mai mulki ta APC a zaɓen da ya gabata. Wannan goyon baya nasa da bai ɓoye ba ya ƙara rikita al’amura a jam’iyyar PDP, inda rikici ya ƙara ƙamari a cikin jam’iyyar.
Rikicin tsakaninsa da shugabancin PDP ya ƙara muni bayan faduwarsa a zaɓen fidda gwani na shugaban ƙasa na jam’iyyar a 2022. Bayan haka kuma, an ƙi zaɓarsa a matsayin abokin takarar Atiku Abubakar, inda aka bawa tsohon gwamnan jihar Delta, Ifeanyi Okowa, tikitin mataimaki, lamarin da ya sabawa shawarar wasu jiga-jigan jam’iyyar.