Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, ya bayyana cewar matsalolin wannan al’umma a fili suke, inda ya bayyana wasu daga cikinsu da kuma hanyar samun mafita.
Malamin ya sanar hakan cikin wani saƙon daya wallafa a shafin sa na Facebook, a daren Litinin.
Yace matsalolin sune;
1. Muna aure ba tare da soyyayya ba.
2. Muna haihuwa ba tare da yin tarbiyya ba.
3. Muna salla ba tare da tsaron Allah ba.
4. Muna koyan ilmi ba tare da aiki ba.
5. Muna magana ba tare da gaskiya ba.
6. Muna daukan alƙawari ba tare da cikawa ba.
7. Muna karɓar amana ba tare da kulawa ba.
8. Muna son kuÉ—i ba tare da Sana’a ba.
9. Muna son Annabi (SAW) ba tare da bin koyarwar sa ba.
10. Muna son Aljannah ba tare da aiki ba.
11. Muna son a amsa mana addu’a ba tare da cin halal ba.
12. Gamu da bala’in son duniya da Æ™in mutuwa.
Daga karshe makamin yace mafita kawai mu tuba mu gyara, muce Allah mun tuba ka yafe mu.