Fiye da maniyyata 2,700 sun rasa damar zuwa hajjin bana – NAHCON

0
249

Hukumar aikin hajji ta ƙasa (NAHCON) ta bayyana cewa fiye da maniyyata 2,700 daga Najeriya ba za su samu damar gudanar da aikin Hajji na shekarar 2025 ba, sakamakon gasa kammala biyan kudin tafiya a cikin wa’adin da aka kayyade.

A cikin wata sanarwa da mataimakiyar daraktan yada labarai na hukumar, Hajiya Fatima Sanda Usara ta fitar, NAHCON ta bayyana cewa duk da kokarinta na neman karin lokaci daga hukumomin Saudiyya domin cigaba da rajistar biza, ba a samu nasara ba.

Sanarwar ta ce daga cikin maniyyata 14,158 da suka yi rajista karkashin kamfanonin yawon bude ido, mutum 13,217 ne kacal aka samar musu da biza.

NAHCON ta nemi afuwa daga wadanda lamarin ya shafa, tana mai jaddada cewa zuwa aikin Hajji kira ne na Ubangiji, kuma kowa da lokacinsa.

Hukumar ta kuma shawarci maniyyata masu niyyar zuwa Hajji a nan gaba da su rika kammala biyan kudinsu da wuri, domin kaucewa irin wannan matsala a gaba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here