Matasan ƴan kasuwa daga Kano sun bayyana yadda ake neman durkusar da kamfanin su

0
138

Wasu matasan yan kasuwa daga jihar Kano, maisuna Zaharaddeen Imam Yahya, da Yusuf Imam Yahaya, sun shaidawa duniya yadda ya kwashe kusan shekaru shida yana fuskantar abinda ya kira rashin adalci, da kuma ƙoƙarin murƙushe kamfaninsa da wasu mutane ke shirin yi.

Zaharaddeen mai shekaru 27 da haihuwa, ya bayyana cewa kamfaninsa dake samar da ganyen shayi na Y&Z ya faɗa cikin rikici da wani babban kamfani da ake kira Top Tea, rikicin da ya samo asali daga tambarin samfurin shayin da kamfaninsa ke sarrafawa duk da a cewar sa sun bi dukkan matakan doka da aka shimfiɗa kafin samun tambarin ganyen shayin nasa.

Mun yi rijista da CAC (Hukumar Rijistar Kamfanoni), mun samu lasisin tambari daga hukumar Trademark bayan an bincika aka tabbatar cewa ba kowa ke da shi ba. Mun kuma samu takardar amincewa daga NAFDAC da SON kafin mu fara sarrafa ganyen shayin, inji shi

Amma yace duk da bin da ƙa’idar da suka yi, suna fuskantar matsin lamba da tsangwama daga wasu mutane masu ƙarfi daga kasar nan waɗanda ke ƙoƙarin durƙusar da harkarsu ta kasuwanci.

Yace bayyana cewa kotu ta yanke hukunci inda ya samu nasara har aka tabbatar da cewa waɗanda suke kai musu farmaki da bita da kulli ba su da hurumin mallakar tambarin da ake ta ja’inja akai.

Ya ƙara da cewa rundunar yansandan Najeriya ta saka sunansu da hotansu a jerin masu laifi da ake nema ruwa a jallo, wanda yace hakan ba daidai bane, domin babu wani mummunan laifi da suka aikata.

Ɗan kasuwar yace wannan batu ba rikici ne na kasuwanci ba, inda yace yana da alaka da yadda ake son take matasa ‘yan Arewa da ke nufin dogara da kansu.

Zaharaddeen yayi gargaɗin cewa idan aka ci gaba da barin irin wannan abu yana faruwa, zai hana matasa tsayawa da kafafunsu a fagen kasuwanci, kuma hakan zai ƙara tsananta fatara da rashin aiki a yankin Arewa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here