Magoya bayan PSG biyu sun mutu a saboda murnar lashe Champion league
Mutane biyu sun rasa rayukansu, yayin da aka kama wasu ɗaruruwan, sannan aka ƙona motoci a daren jiya, Asabar yayinda magoya bayan kungiyar Paris Saint-Germain (PSG) ke murnar nasarar da suka samu a gasar cin kofin zakarun Turai.
Lamarin ya faru a babban wurin taruwar magoya bayan PSG dake birnin Paris, na ƙasar Faransa, inda aka cika da murna, raira wakoki bayan PSG ta lallasa Inter Milan da ci 5-0 a Munich.
Mahukuntan Faransa sun bayyana cewa an kama mutane 491 a babban birnin Paris, lokacin da dubban mutane suka mamaye titin Champs-Elysees, inda rikici ya barke tsakaninsu da jami’an tsaro.
A fadin kasar gaba daya, ciki har da Paris, adadin wadanda aka kama ya kai 559.
Haka kuma, an tabbatar da mutuwar mutane biyu.