Buhari ya karrama dan sandan da yaki karbar cin hanci a Kano

0
95

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya jinjinawa wani baturen ‘yan sandan kasar, SP Daniel Itse Amah dake aikin DPO a Nasarawa dake jihar Kano, saboda yadda yaki karbar cin hancin Dala dubu 200 dangane da wani bincike da yake akan fashi da makami.

Buhari ya karrama DPOn wajen taron yaki da cin hanci da rashawar da Hukumar ICPC ta shirya domin tattauna batutuwan da suka shafi cin hancvi da rashawa a tsakanin ma’aikatan gwamnati.

SP Amah ya nuna kwarewa da kuma kyamar cin hanci lokacin da ya gudanar da aikin sa na kama wani da ake kira Ali Zaki da wasu jami’an ‘yan sanda dangane da fashin kudin da ya kai naira miliyan 320.

Kafin wannan lokaci, Sufeto Janar na ‘yan sandan kasar Alkali Baba ya yawaba DPOn saboda abinda ya kira kwarewarsa da jajircewa da kuma nuna bajinta wajen gudanar da aiki.

Shugaban Hukumar ICPC Farfesa Bolaji Owasanoye ya bukaci hadin kan jama’a domin ganin an dakile ayyukan cin hanci a tsakanin al’ummar Najeriya.