An nemi Hamdiyya Sidi Sharrif, an rasa wadda itace Gwamnatin Jihar Sokoto ke shari’a da ita kan zargin yunkurin tada zaune tsaye a jihar.
Lauyan dake kare Hamdiyya, Abba Hikima Fagge, ne ya bayyana hakan a shafinsa na Facebook, inda ya ce ta bace tun a jiya Talata, Lokacin da ta fita siyan kayan miya da misalin karfe 10 na safe, kuma ba a sake ganin ta ba har zuwa wannan loakci.
A yau ne ake sa ran za a ci gaba da sauraren karar su da Gwamnatin Jihar Sokoto, sai dai lauyan ya ce tuni suka sanar da rundunar ‘yan sandan jihar Sokoto game da lamarin É“acewar tata.