Hukumar aikin hajji ta ƙasa NAHCON ta kammala jigilar mutane 32,549, daga cikin maniyyatan hajjin bana, wanda hakan ya ke a matsayin kaso 79.1 na ɗaukacin maniyyan kasar nan.
Anyi jigilar wadannan mutane a cikin sahu 79 na jirgi da aka fara jigilar daga ranar 9 ga watan Mayu zuwa yanzu.
Mataimakiyar daraktan yaɗa labaran hukumar Fatima Sanda Usara, tace tuni aka kammala kwashe maniyyatan jihohi da dama wanda suka haɗa da Adamawa, da Filato, yayin da jihohin Bauchi da Gombe da Jigawa da Abuja zasu kammala jigilar mutanen su a yau Laraba, sai Kano da Kwara da zasu biyo baya a shirin kammala jigilar.