Sarkin Daura ya cire Dagaci akan zargin yin fyade da garkuwa da mutane
Mai martaba sarkin Daura Alhaji Faruq Umar Faruq, ya cire Iliya Mantua daga muƙamin sa na dagacin Mantua, bisa zargin sa da aikata laifin yin fyade da garkuwa da mutane, a ƙaramar hukumar Baure.
Sanarwar da Masarautar ta fitar a ranar Litinin, tace ba za’a lamunci duk wani nau’in cin zarafi ko take hakkin a’lummar ta ba.
Dakatarwar ta biyo bayan zanga-zangar da a’lummar yankin Yarmalulu, suka gudanar kan zargin dagacin da yin garkuwa da wata mata mai suna Zulaihat da jaririn ta, tare da neman kuɗin fansa naira miliyan 20 da kuma yin fyade.
Sarkin ya roƙi al’umma su cigaba da bawa mahukunta bayanai don bankaɗo masu laifi tare da hukunta su.