Jam’iyyar PDP za ta kira taron gaggawa domin ceto takarar Atiku

0
108

Idan ba a canza tunani ba, jam’iyyar PDP za tayi zaman a musamman a makon nan, a dalilin irin rigingimun da suke bijiro mata har gobe.

Punch tace majalisar amintattu watau BoT za tayi taro nan da ‘yan kwanaki kadan da nufin a shawo kan rikicin gida saboda a lashe zabe mai zuwa.

Wannan taro yana cikin kokarin da ake yi saboda a magance barakar da za a iya samu wajen takarar Atiku Abubakar a zaben neman shugaban kasa.

Da aka tattauna da tsohon shugaban BOT, Sanata Walid Jibrin ya shaidawa ‘yan jarida abubuwan da ke faruwa sun dame su domin sun ki zuwa karshe.

“Akwai taron BoT a makon nan, amma ban san ranar ba tukuna. Abin da muke so shi ne mu ga muna magana da murya daya.

Sannan mu tsaya a kan tsare-tsare da kuma manufofin da za su taimaka mana wajen lashe zaben shugabancin kasa na 2023.

Dole ne mu hada-kan ‘ya ‘yanmu, su jawo mutanen Najeriya domin su fito su zabi Atiku Abubakar da Gwamna Ifeanyi Okowa.”

Babu mamaki a wannan zama da za ayi, BoT za ta dauki matsaya a kan Sanata Iyorchia Ayu wanda ‘yan bangaren Wike suka huro wuta ya yi murabus. Walid Jibrin ya kuma yi Allah-wadai da sabanin da ake samu tsakanin ‘yan majalisar NWC.

Ana sa ran kwamitin sulhu zai hada Nyesom Wike a yau.