Yan kasuwar fannin fetur sun bayyana damuwa akan yadda suke gaza samun man fetur daga matatun man fetur na Fatakwal da Warri, shekara guda bayan sanar da cewa an gyara su.
Matatun man na Fatakwal da Warri sun kasance mallakin gwamnatin tarayya da aka sanar da cewa sun dawo aiki yadda ya kamata bayan laƙume maƙudan kudaden gyara.
Ƙasar nan ta kashe kimanin dala biliyan 2.4 tun daga shekara 2021 domin farfaɗo da waɗannan matatun da ke yankin Niger Delta, da nufin dakatar da dogaro da shigo da man fetur daga ƙasashen waje, Sai dai har yanzu, ba su fara fitar da man fetur ba.
Kungiyar ‘yan kasuwa masu gidajen mai ta Æ™asa, PETROAN, ta bayyana wa kamfanin dillancin labaran Reuters cewa sama da mambobinta 6,700 har yanzu na dogaro da shigo da mai daga waje da kuma matatar Dangote.
Bisa bayanan ƙungiyar, har zuwa watan Maris babu wani fetur da aka fara fitarwa daga matatar Fatakwal wadda a baya ita ce matata mafi girma a kasar nan.
Kungiyar PETROAN ta buƙaci a bayyana gaskiya game da halin da matatun ke ciki, tana mai cewa, yan Najeriya na son sanin gaskiyar ranar da za a kammala gyaran matatun.