Shugaban sojojin Sudan Janar Abdel Fattah Al-Burhan, ya naɗa sabon Firaminista, tun bayan da aka yiwa ƙasar juyin mulki a shekarar 2021.
Bugu da ƙari har yanzu babu wani cikakken bayanin irin ƙarfin ikon da firaministan Kamil Idris, ke da shi, a wannan sabon muƙamin da aka naɗa shi, kasancewar har yanzu ƙasar ta Sudan na fama da yaƙin da ta ke yi da dakarun RSF
Da jimawa dai janar Burham na ƙoƙarin kafa sabuwar gwamnati tun bayan da dakarun gwamnati suka sake ƙwato babban birnin ƙasar Khartoum a watan Maris da ya gabata.
Dakarun na RSF sun kai hare-hare da dama ta hanyar amfani da jirage marasa matuƙa inda suka haifar da tarnaƙi ga lamurran da suka shafi ayukkan gwamnati musamman a manyan biranen ƙasar.