Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf, ya rantsar da AVM Ibrahim Umaru, a matsayin sabon kwamishinan ma’aikatar tsaron cikin gida.
Gwamna Abba, ya rantsar da kwamishinan yayin taron majalisar zartarwa karo na 28 daya gudana a yau Litinin, wanda akayi a gidan gwamnatin jiha na rukunin gidajen kwankwasiyya.
Kafin naÉ—in nasa AVM Ibrahim Umaru ya kasance daraktan ayyuka na musamman a gidan gwamnatin Kano, sannan yayi aiki da rundunar sojin sama.