Mayaƙan Boko Haram da ISWAP sun yi ajalin manoman jihar Borno 90 cikin watanni 5 suka shuɗe.
A baya-bayan nan kungiyoyin biyu suka kashe manoma kimanin 50, yawancinsu ta hanyar kisan gilla, kuma hanr yanzu an kasa dauko gawarwakin, a Kamarar Hukumar Kukawa.
Mayakan sun kuma yi garkuwa da wasu da dama baya ga wadanda suka tsallake rijiya da baya a hare-hare.
Majiyoyin tsaro sun tabbatar da cewa kungiyoyin ‘yan ta’addan sun kai hare-haren ne a tsakanin watan Janairu zuwa Mayun da muke ciki.
Hari na baya-bayan nan shi ne wanda mayakan kungiyar ISWAP suka ritsa manoman da ke aiki a gonakin wake suka yi wa mutum 50 kisan gilla a yankin Karanti da ke Karamar Hukumar Kukawa a ranar Alhamis, 15 ga watan Mayu.
A gefe guda kuma, mayakan kungiyar Boko Haram da basa yin shiri da ISWAP sun kai wani hari garin Baga, inda suka yi wa masu kamun kifi da manoma kisan gilla.