Gwamna Uba Sani, na Jihar Kaduna yace baƙin talauci da lalacewar al’amuran tattalin arziki ne dalilan da suka ta’azzara matsalolin da arewacin Najeriya ke ciki, sannan yace yankin zai cigaba da fuskantar tashin hankali in aka gaza ɗaukar matakin gyara matsalolin.
Uba Sani, ya bayyana hakan a ranar Lahadi data gabata lokacin da ake zantawa dashi a shirin siyasa na tashar talabijin ta Channels.
Haka ne yasa gwamnati na ta fara aiki akan fito da hanyoyin rage talauci da samar da ayyukan yi tsakanin matasa, inji gwamnan.
Yace fiye da kashi 60 zuwa 65 cikin ɗari na mutanen arewacin Najeriya musamma waɗanda ke rayuwa a arewa maso yamma na fama da tsananin talauci a lokacin da ya zama gwamman jihar Kaduna.
Uba Sani ya ce hakan na iya sa matasa da dama shiga kungiyoyin ta’addanci kasancewar ƴan bindiga za su iya ɗaukar su haya domin kai hare-hare sannan a basu kuɗi.