Shugaban ƙasa Tinubu ya bayar da umurnin cigaba da haƙo fetur a arewa
Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya bayar da umurnin a cigaba da aikin haƙo ɗanyen man fetur a yankin Kolmani dake kan iyakokin Bauchi da Gombe a arewacin kasar nan.
Ƙaramin Ministan mai na Heineken Lokpobiri ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin sadarwa, Nneamaka Okafo ya fitar ranar Lahadi .
A cewar Lokpobiri, Shugaba Tinubu ya amince a bayar duk damar data rage domin ci gaba da aikin haƙo man.
Ya kuma sanar da cewa gwamnatin tarayya ta samar da wata cibiyar nazarin albarkaun man fetur da iskar gas a ƙaramar hukumar Alƙaleri da ke jihar Bachi domin tabbaar da samun nasarar cigaba da aikin.
A watan Nuwamban 2022 ne aka fara aikin shirin haƙar mai na Kolmani.
A makon da ya gabata shugaban kamfanin mai na ƙasa, Bayo Ojulari ya shaida wa BBC cewa kamfanin NNPCL zai ci gaba da aikin tono mai a Kolmani.