Saudiyya ta ɗauki nauyin Falasɗinawa 1000 don yin aikin Hajjin bana

0
117

Saudiyya ta ɗauki nauyin Falasɗinawa 1000 don yin aikin Hajjin bana

Hukumar kula da Masallatan Harami guda biyu, karkashin jagorancin Sarki Salman bin Abdulaziz Al Saud, na ƙasar Saudiyya ta bayar da umarnin daukar nauyin Falasɗinawa dubu daya don gudanar da aikin Hajjin bana.

Falasɗinawan da za’a ɗauka don yin aikin Hajjin sun haɗar da maza da mata, kuma za’a basu dukkanin kulawar da ta dace.

Sarki Salman, shine zai biya kudin da za’a kashewa Falasɗinawan, kamar yadda shafin Inside the Haramain, ya bayyana a yau Litinin.

Dama gwamnatin Saudiyya ta saba ɗaukar nauyin Falasɗinawa don gudanar da aikin hajji a shekara daban daban, don faranta musu rai da sauƙaƙa musu ƙuncin rayuwa sakamakon yaƙin da Isra’ila keyi dasu tare da take hakkin su.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here