Hukumar tace fina-finai ta jihar Kano ta dakatar da wasu fina-finai 22 masu dogon zango, wanda suka hadar Dakin Amarya, Labarina, Gwarwashi, Dadin Kowa, Gidan Sarauta and Manyan Mata.
Jerin jadawalin fina-finan sun ƙunshi;
1. Dakin Amarya
2. Mashahuri
3. Gidan Sarauta
4. Wasiyya
5. Tawakkaltu
6. Mijina
7. Wani Zamani
8. Labarina
9. Mallaka
10. Kudin Ruwa
11. Boka Ko Malam
12. Wayasan Gobe
13. Rana Dubu
14. Manyan Mata
15. Fatake
16. Gwarwashi
17. Jamilun Jiddan
18. Shahadar Nabila
19. Dadin Kowa
20. Tabarmar
21. Kishiyata
22. Rigar Aro
Bayanin hakan na cikin wata sanarwar da hukumar ta fitar a yau Litinin 19 ga watan Mayu, dauke da sanya hannun jami’in yaɗa labaran ta, Abdullah Sani Sulaiman, inda yace fina-finan, sun saɓawa dokokin da ya kamata ace sun bi kafin al’umma kalla.
A cewar sanarwar shugaban hukumar tace fina-finai ta jihar Kano Abba El-Mustapha, ne ya bayar da umurnin hakan bayan gudanar da taron masu ruwa da tsaki.
Hukumar ta nemi tallafin tashoshin talabijin da hukumar kula da kafafen yada labarai NBC, su bada gudunmawa wajen tabbatar da wannan umarni.