Mayaƙan ISWAP sun kashe manoma da masu kamun kifi a Borno

0
65

Mayaƙan ISWAP sun kashe  manoma da masu kamun kifi a Borno

Mayaƙan kungiyar ƴan ta’addan ISWAP sun kashe manoma da masu kamun kifi su 23 a jihar Borno.

Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru da sanyin safiyar Alhamis data gabata a yankin Malam Karanti dake kusa da Baga a ƙaramar hukumar Kukawa.

Ɗan jarida mai Sharhi akan harkokin tsaro Zagazola Makama, ya wallafa a shafin sa na X, a yau asabar cewa mafi yawancin mutanen da aka kashe sun fito ne daga Gwoza, wanda kafin kisan nasu sun ƙulla yarjejeniya da Boko Haram akan cewa zasu riƙa biyan mayaƙan haraji don yin noma da kamun kifi ba tare da mayaƙan sun kashe su ko kai musu hari ba, sai dai mayaƙan ISWAP masu rikici da tsagin Boko Haram sun ƙalubalanci yarjejeniyar.

Kamar yadda bayanai suka nuna mayaƙan ISWAP sun farmaki manoma da masu kamun kifin da misalin karfe 9 na safiyar Alhamis, tare da yanka 23 daga cikin su, bayan  zargin cewa mutanen sun haɗa kai da yan Boko Haram da kuma bijirewa umarnin ISWAP mai iko da yankin na Malam Karanti.

Wata majiya tace wani tsoho ɗaya ne ya tsira daga harin, kuma shine ya sanar da faruwar lamarin.

Har ila yau, mayaƙan sun buɗe wuta akan mutanen da suka je ɗauko gawarwakin mamatan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here