Gwamnatin Kano ta haramta bikin Kauyawa Day

0
112

Hukumar Tace Fina-finai da Dab’i ta Jihar Kano ta sanar da haramta gudanar da Bikin “Kauyawa Day” a fadin jihar, tare da fitar da matakai guda shida da za su tabbatar da bin wannan doka da kuma cikar manufofin da aka sanya a gaba.

A wata sanarwa da Jami’in hulda da jama’a na hukumar, Abdullahi Sani Sulaiman, ya fitar, an bayyana cewa shugaban hukumar, Abba El-mustapha, ya gabatar da matakan ne a wani taron manema labarai, inda ya jaddada cewa manufar wannan mataki ita ce kare tarbiyyar al’umma da tabbatar da zaman lafiya.

Matakan da za’a ɗauka sune Kamar haka;

1. Dakatar da dukkan dakunan taro da gidajen bukukuwa (event centers) daga karbar shirye-shiryen da suka shafi Bikin “Kauyawa Day” har sai an kammala sabunta dokokin da suka shafi irin wadannan taruka.

2. Yin hadin gwiwa da manyan jami’an tsaro na gwamnati domin tabbatar da bin doka da oda.

3. Hada kai da jami’an ‘yan kato da gora (Vigilante) da kuma hukumar Hisbah domin tabbatar da bin umarnin doka.

4. Tattaunawa da dattawan unguwanni da kungiyoyin matasa domin wayar da kai da kuma samun goyon baya.

5. Hadin gwiwa da kungiyar limamai da majalisun malamai na jihar domin fadakar da iyaye da shugabannin al’umma.

6. Hada hannu da masu unguwanni, dagatai da hakimai domin karfafa matakin a kowane mataki na al’umma.

Hukumar ta bayyana kudirinta na ganin an tsaftace harkokin nishadi a jihar, tare da tabbatar da cewa duk wani abu da zai iya kawo cikas ga tarbiyya da zaman lafiya ba zai samu wuri ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here