Ɗaukacin a’lummar Gaza sun rasa muhallin su a yaƙin Isra’ila

0
164

Wani rahoton da majalisar dinkin duniya ta fitar ya nuna cewa rikicin yaƙin da ke faruwa tsakanin Isra’ira da yankin Gaza ya sanya kaso 90 zuwa 100 na a’lummar yankin sun rasa muhallin su daga farkon yaƙin zuwa yanzu.

Da farko dai Isra’ila ta kori mutanen Gaza zuwa kudu da inda suke rayuwa, wanda bayan haka sojojin Isra’ila ke riƙe da ikon yankunan da ta kori Falasɗinawan.

Hukumar Majalisar Dinkin Duniya da ke kula da ‘yan gudun hijirar Falasdinawa (UNRWA) ta ce da dama daga cikin waɗanda aka tilasta wa barin gidajensu sun kasance suna yin hijira sau 10 ko fiye da haka.

Ta kuma ƙiyasta cewa tun daga ranar 18 ga Maris, lokacin da Isra’ila ta kawo ƙarshen zaman lafiya na watanni biyu ta kuma dawo da hare-haren ta a Gaza, aƙalla mutum 430,000 ne hare-haren ya sake tilasta wa yin hijira.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here