Shugaban ƙasa, Bola Tinubu ya amince da kafa sabuwar rundunar tsaron dazuka, domin yaƙar ƴan ta’addan dake samun mafaka a dazukan.
A karkashin wannan shiri, za a ɗauki sama da masu tsaro 130,000 da za su kasance da kayan yaƙi da horo na musamman domin kare dazukan ƙasar nan guda 1,129.
Bayanin hakan na cikin wata sanarwar da ta fito daga mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin yaɗa labarai da hulɗa da jama’a, Sunday Dare, wanda ya wallafa ta a shafinsa na X.
Sanarwar ta ce wannan mataki na tsaro an amince da shi ne yayin taron majalisar zartarwa ta tarayya da aka gudanar ranar Litinin.
Shugaba Tinubu ya umurci kowace jiha da ta ɗauki ma’aikata tsakanin 2,000 zuwa 5,000 domin zama masu tsaron daji.
Ofishin mai ba da shawara kan harkokin tsaro na ƙasa da kuma ma’aikatar kula da muhalli ne za su sa ido kan aikin ɗaukar masu tsaron da horar da su domin tabbatar da cewa sun samu cikakken shiri da kayan aiki na zamani da ya kamata.
Babban aikin da ake sa ran masu tsaron dajin za su yi shi ne fatattakar masu tayar da ƙayar baya da ɓata gari da suka fake a cikin dazuka suna aikata laifuka.