Mataimakin gwamnan Kano Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo, da sarkin Kano Muhammadu Sunusi II, sun ƙaddamar da tashin jirgin farko na maniyyata Hajjin bana daga jihar Kano a yau Laraba.
An ƙaddamar da tashin maniyyatan a filin tashi da saukar jiragen sama na Malam Aminu Kano, wanda jirgin Max Air, ya ɗauke su.
Tuni dai maniyyatan sun bar gida Najeriya, inda zasu sauka a ƙasa birnin Madina.