Sojoji sun lalata haramtattun matatun man fetur 9

0
77

Dakarun rundunar sojin ruwa ta kasa sun samu nasarar lalata haramtattun matatun man fetur 9, tare da bankaɗo man fetur da aka tace wanda yawan sa yakai lita 175,000, a yankin Ogba/Egbema/Ndoni, dake jihar Rivers.

Sanarwar da rundunar sojin ruwan ta fitar ta bayyana cewa an samu ɗimbin kayan aikin da ake amfani dasu wajen tace man, da tankunan adana mai 30 wanda ke ɗauke da ɗanyen man sata da yawan sa yakai lita dubu 60, sai lita dubu 80 na Gas da Kalanzir lita dubu 33.

Kwamandan rundunar, Commodore Cajethan Aniaku, yace an samu nasarar yin wannan aiki a ranar 12 ga watan Mayu da muke ciki, kamar yadda ya bayyana cikin sanarwar da aka rabawa manema labarai a birnin Fatakwal da daren Talata.

Commodore Cajethan Aniaku, yace wannan yunkuri na daga cikin kokarin da rundunar sojin ruwan keyi wajen dakile satar danyen man fetur a Najeriya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here