China da Amurka zasu zaftarewa junan su haraji

0
85

Kasashen China da Amurka sun fara aiwatar da yarjejeniyar daidaita yaƙin kasuwancin da suka faro bayan hawan Donald Trump, karagar mulkin Amurka.

Zuwa yanzu dai an fara samun sassauci a tsamin alaƙar kasuwancin kasashen.

Hukumar shige da fice ta China ta sanar da fara aiki da yarjejeniyar da aka cimma da masu shiga tsakani, a karshen makon da ya gabata, wanda tuni itama Amurka ta fara zartar da yarjejeniyar daidaita batun kasuwancin.

Wannan ne karon farko da bangarorin biyu, suka amince su sassautawa kansu bayan shafe watanni suna ja in ja, kuma dukkan bangarorin biyun sun amince su zaftare kashi 115 na harajin da suka ƙaƙabawa kansu.

Yarjejeniyar ta kwanaki 90 za ta ba da damar tattaunawa don cimma yarjejeniya yadda ya kamata.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here