Za’a tura ƙarin sojoji zuwa Yobe da Borno

0
88
Sojojin Najeriya
Sojojin Najeriya

Majalisar dattawa ta amince da bukatar tura karin jami’an sojoji jahohin Borno da Yobe domin yaki da mayakan Boko Haram wadanda ke ci gaba da zafafa hare-hare a kwanan nan, inda suka kashe sojoji da dama a kananan hukumomin Marte da Monguno dake jihar Borno.

Wannan dai na faruwa ne bayan wani kuduri da Sanata Muhammed Tahir Monguno dan majalisar dattawa mai wakiltar Borno ta arewa, ya gabatar a gaban majalisar.

Sanatan ya ce ya gabatar da kudurin ne ganin yadda matsalar tsaron take neman sake komawa kamar baya.

Ya ce a lokacin da ake tsananin fama da Boko Haram wajen kashi biyu cikin kashi uku na kananan hukumomin jihar Borno suna karkashin ikon kungiyar Boko Haram.

Boko Haram na rike da kananan hukumomin, sun kori hafsoshinmu, su ke rike da ikon duka wadannan yankuna,” inji shi.

Danmajalisar dattawan ya kara da cewa, to amma bayan wani lokaci gwamnati ta tashi tsaye an bayar da duk wani abu da ake bukata har sojoji suka yi nasarar korar Boko Haram daga wadannan yankuna.

Ya kara da cewa matsalar tana neman dawowa ne, saboda ‘yan Boko haram sun fahimci cewa an kwashe yawancin sojoji da kayan aiki an mayar da su yankin arewa maso yamma inda ake fama da matsalar tsaro ta barayin daji.

Shafin BBC, ya rawaito cewa dan majalisar ya ce wannan shi ya sa mayakan Boko Haram suka fahimci haka shi ya sa yanzu suka samu damar kai hare-hare inda a cikin ‘yan kwanakin nan suka kai hari sansanin soji da ke Marte da kuma Gajiram.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here