Babbar kotun tarayya dake Abuja, ta saka ranar 27 ga watan Yuni na wannan shekara a matsayin lokacin da zata yanke hukunci kan shari’ar da Sanata Natasha Akpoti Uduaghan, ta shigar akan dakatarwar da aka yi mata daga Majalisar dattawa.
Mai shari’a Binta Nyako, ce ta sanya ranar, bayan Æ™arar da Natasha ta shigar da majalisar kan dakatarwar da akayi mata karkashin jagorancin shugaban majalisar dattawa Godswill Akpabio, biyo bayan zargin ta da saÉ“a dokokin majalisar.
Waɗanda ake ƙara sune majalisar dokokin ƙasa, shugaban majalisar dattawa da Sanata Neda Imasuen, wanda ya jagoranci kwamitin ladabtawar daya dakatar da Natasha.
Natasha dai itace ke wakiltar mazaɓar Kogi ta tsakiya.