Ƙarancin samun maki a jarrabawar JAMB yasa wata ta kashe kanta

0
166

Ƙarancin samun maki a jarrabawar JAMB yasa wata yar shekara 19 ta kashe kanta, ta hanyar cin shinkafar ɓera.

Ɗalibar mai suna Opesusi Faith Timilehin, ‘yar asalin jihar jihar Ogun, sannan mazauniyar yankin Odogunyan dake Ikorodu a Jihar Legas, ta samu maki 190, a JAMB sai dai makin yayi kaɗan a irin karatun da take son yi a jami’a, da hakan yasa ba zata samu gurbin karatun da take buƙata ba.

Rahotanni sun bayyana cewa mazauna unguwar da Timilehin, ke rayuwa sun yi alhinin rasuwar ta, tare da bayyana ta a matsayin mai hankali.

Ɗaya daga cikin danginta ya ce Timilehin ta nemi gurbin karatu a  sashin Microbiology, kuma ta sake rubuta wannan jarabawar a karo na biyu bayan ta zauna a shekarar da ta gabata, wanda sakamakon baya yafi na yanzu kyau.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here