Gwamnatin jihar Kano, ta shelanta aniyar ta, ta samar da cigaba a wasu makarantu 200, ta hanyar sanya musu wutar lantarki mai amfani da hasken rana, da kuma samar da na’ura mai ƙwaƙwalwa 250 a kowace daga cikin makarantun 200.
Gwamnatin zata yi wannan aiki karkashin shirin bankin duniya na tallafin AGILE.
Kakakin gwamnan Kano Sunusi Bature Dawakin Tofa, ne ya sanar da hakan, yana mai cewa wannan wani bangare ne na sake farfaɗo da fannin ilimin jihar Kano.
Gwamna Yusuf, ya bayyana hakan yayin kaddamar da rabon kayan koyarwa ga makarantun Firamare da na Sakandare da aka gudanar a Kano.
Gwamna Abba, yace samar da wutar lantarki mai amfani da hasken rana zai bawa makarantu damar samun wuta mai dorewa, wanda hakan zai taimaka wajen inganta yanayin koyarwa zamanance.
Daga ɓangaren na’ura mai ƙwaƙwalwar da za’a raba kuwa, ana kyautata zaton zasu ƙarfafa koyar da ilimin kimiyya da fasaha a makarantun gwamnati, don cike giɓin da ake da shi a bangaren koyar da ya’yan talakawa harkokin fasaha.