Gwamnatin Kano zata bawa malamai bashin ababen hawa

0
99
Abba Gida-Gida
Abba Gida-Gida

Gwamnatin Kano zata kashe Naira miliyan 200 wajen siyo ababen hawan da zata rabawa malaman makarantun firamare da sakandire bashi.

Gwamna Abba Kabir Yusuf, ne ya amince a fitar da kuɗaɗen da kuma sayo ababen hawan don sauƙaƙawa malaman.

Bayanin hakan na cikin wata sanarwar da kakakin gwamnan Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar inda yace samar da ababen hawan ga malaman wani mataki ne na inganta jin dadin ma’aikata da ƙara musu kwarin gwuiwa a aikin su na koyarwa.

Gwamna Yusuf ya bayyana hakan a lokacin bikin kaddamar da rabon kayan koyarwa ga makarantun gwamnati, a wani bangare na sake fasalin ilimi. Gwamnatin ta jihar Kano tace ta kashe kuÉ—aÉ—en da yawan su yakai Naira biliyan 2 wajen siyo kayayyakin karatun da aka raba.

Gwamna Yusuf, ya jaddada kudirinsa na inganta samar da ababen more rayuwa musamman a bangaren da ya shafi ilimi, inda ya bayyana malamai a matsayin ginshikin ci gaban kowacce al’umma.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here