Tattalin arzikin Najeriya ya inganta a karkashin mulkin Tinubu—Bankin duniya

0
157
Tinubu

Bankin Duniya ya sanar da cewa tattalin arzikin Najeriya ya haɓɓaka fiye da kowanne lokaci cikin shekara goma da ta gabata, sakamakon wasu muhimman gyare-gyaren da gwamnati mai ci ta aiwatar. Sai dai Bankin yace hauhawar farashin kayayyaki na ci gaba da addabar a’lumma.

Bayanin hakan na cikin wata sanarwa da Bankin ya fitar ga manema labarai, inda ya bayyana cewa ƙarfin tattalin arziƙin Najeriya na cikin gida ya ƙaru da kashi 4.6 cikin 100 a zangon ƙarshe na shekarar 2024.

Rahoton ya danganta hakan ga cigaban da ake samu a ɓangaren man fetur da iskar gas, da kuma ƙaruwar zuba jari da bunƙasar fasahar zamani da harkar kudi.

Amma bankin yace ɓangaren noma ya ci gaba da samun tangarɗa, inda ya karu da kashi 1.2 cikin 100 kacal a shekarar 2024.

Bankin Duniya ya yaba wa gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu saboda ɗaukar matakan gyaran tattalin arziki tun bayan hawansa mulki a watan Mayun 2023.

Daga cikin wadannan gyare-gyare akwai cire tallafin man fetur.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here