Ambaliyar ruwa: Gwamnatin Yobe ta ba da umarnin kwashe al’ummar garuruwa 2

0
89

Gwamnatin Yobe ta ba da umarnin kwashe mutanen Usur da Gasma da ambaliyar ruwa ta yi wa barazana a kananan hukumomin Bade da Karasuwa.

Mataimakin gwamnan jihar, Alhaji Idi Gubana ne ya bayar da wannan umarni a jiya Lahadi a Gashua lokacin da ya ziyarci yankunan da ambaliyar ruwa ta shafa.

Ya umurci Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta Jihar (SEMA) da ta kwashe mazauna Usur da Gasma zuwa sabon rukunin gidaje da aka gina a Jaji Maji.

Mataimakin gwamnan ya ce sun kai ziyarar ne domin jajantawa wadanda ibtila’in ya rutsa da su da kuma tantance irin ɓarnar da aka yi domin samun tallafin da ya dace.

Gubana ya kuma umurci SEMA da ta samar da kayan agaji ga wadanda abin ya shafa domin rage musu raɗaɗi.

A nasa jawabin, Sarkin Bade, Alhaji Abubakar Suleiman, ya gode wa mataimakin gwamnan bisa ziyarar jaje.

Ya kuma bukaci al’ummar garuruwan da su yi addu’ar Allah ya dawo da zaman lafiya a yankunan da lamarin ya shafa.

Mataimakin gwamnan ya samu rakiyar kakakin majalisar dokokin jihar Yobe, Alhaji Ahmad Mirwa da sakataren gwamnatin jihar, Alhaji Baba Wali da dai sauransu.