Jami’ar MAAUN ta rufe gidan kwanan daliban ta mata 

0
76

Hukumar gudanarwar Jami’ar Maryam Abacha American University of Nigeria (MAAUN) ta ba da umarnin gaggawa na rufewa tare da janye amincewa da gidajen kwanan dalibai mata na Al-Ansar Indabo da ke unguwar Hotoro da titin UDB a birnin Kano.

Wata sanarwa da Mataimakin Shugaban Jami’ar mai kula da harkokin Dalibai, Dr. Hamza Garba, ya fitar a ranar Lahadi, ta bayyana cewa matakin rufe gidajen kwanan wani bangare ne na kokarin da jami’ar ke yi domin tabbatar da kwanan dalibai cikin aminci, tsaro, tsafta, da kuma ci gaba da nuna matsayinta na kin yarda da duk wata dabi’a ta lalata daga kowanne ɗalibi.

Sanarwar ta kara da cewa, ɗaukar matakin ya zama dole saboda rashin bin ka’idoji da dokokin da jami’a ta shimfida dangane da tafiyar da gidajen kwana masu zaman kansu.

Wasu daga cikin dalilan rufe gidajen sun ƙunshi aikata alfasha daga ɗalibai mata, rashin ruwa da lantarki, yawo cikin dare, tare da yin amfani da wasu nau’in kayan more rayuwa tare da mutanen da ba dalibai ba, inda jami’ar tace hakan na da hatsari ga lafiyar daliban.

MAAUN ta yi amfani da wannan sanarwa wajen umartar daliban ta mata dake waɗancan gidaje akan su gaggauta fita da zarar sun kammala jarrabawa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here