Ƙungiyar IPOB ta saka dokar zaman gida a ɗaukacin jihohin Kudu maso gabas

0
52

Haramtacciyar kungiyar masu rajin kafa kasar Biapra (IPOB) ta bayar da umurnin zaman gida ga ɗaukacin a’lummar Kudu maso gabas.

Ƙungiyar tace za’a yi wannan zaman gida data ayyana a matsayin sadaukarwa ga jaruman kungiyar wanda suka rasa rayukansu a kokarin cikar burin kafa kasar Biapra, a yayin yaƙin basasa da bayan yaƙin.

Ranar Juma’a 30 ga watan Mayu shine lokacin da IPOB ta sanar da cewa babu fita kasuwanni, ko zuwa wani waje a yankin na Kudu maso gabas baki ɗaya.

Bayanin hakan na cikin wata sanarwar da sakataren yaɗa labaran IPOB Emma Powerful, ya fitar a yau Litinin, yana mai cewa umarnin zaman gidan zai fara aiki daga ƙarfe 6 na safe zuwa 6 na yammacin ranar.

Dama ko a baya kungiyar IPOB ta saba tilastawa a’lummar wasu jihohin Kudu maso gabas, yin zaman gida na dole bisa wasu hujjojin su, wanda hakan ke hanyo asarar dukiya da rayuka.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here